A cewar Medicalnewstoday, Herpetic whitlow, ko ɗan karkare yatsa, cuta ce mai raɗaɗi ta hanyar ƙwayar cuta ta herpes simplex (HSV). Yana tasowa lokacin da nau’in HSV ya shiga cikin fata a kusa da yatsa, musamman ma babbar yatsa kuma wani lokacin yana iya samuwa a kan yatsan kafa, sau da yawa ta hanyar ɗan yanka a cikin fata. Ciwon yana haifar da jajaye fata, ciwo, da maruru mai cike da ruwa.
Anan akwai hanyoyi guda 6 don kula da Dan karkare whitlow;
- Ta hanyan Rufe wajan da cutan ta kamuwa : Rufe wurin da abin ya shafa a hankali yana taimakawa wajen hana cutar yaduwa.
- A guji fasa ruwan da ya taru : Kada ku taɓa buɗe ko zubar da ruwan marurun, saboda hakan na iya yaɗa ƙwayar cuta ko barin wurin a buɗe zai sa ki kamu da wata cutan ta biyu.
- Wanke hannaye: Yin haka akai-akai da kyau yana da mahimmanci, musamman kafin da kuma bayan an taɓa wani yanki na Dan karkare . Waɗanda ke aiki a fannin likitanci ko likitan haƙori yakamata su ɗauki kowane mataki, kamar yin aiki da safar hannu a duk lokacin da zai yiwu.
- Gujewa ruwan tabarau: Yin amfani da ruwan tabarau a lokacin da ake fama da Dan karkare na iya yada kwayar cutar zuwa idanu. A sanya tabarau har sai alamun sun warware.
- A guji taba marurun: Wannan wata muhimmiyar hanya ce ta kiyaye kwayar cutar daga yaduwa.
- Faɗa wa likita ko likitan haƙori: sannar da likitocin kiwon lafiya game da cutar zai iya tabbatar da cewa sun yi amfani da matakan kariya masu dacewa.
Daga: Firdausi Musa Dantsoho