Lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka, ya faru ne a cocin da ke da nisan kasa da mita 200 daga fadar Olowo na Owo.
Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Bu hari (mai ritaya), yayin da yake mayar da martani kan lamarin, ya bayyana cewa kasar ba za ta mika wuya ga miyagu ba.
Da yake marawa Buhari baya, Osinbajo ya ce, “Ina tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin yin Allah wadai da kakkausar murya, kisan gillar da aka yi wa masu ibada a ranar Lahadi a cocin St Francis Catholic Church, dake titin Owa-luwa, a masarautar Owo, a jihar Ondo.
“Wannan abin bakin ciki ne da ba za a iya bayyana shi ba, kuma na yi alhinin wadanda suka mutu daga wannan mummunan lamari. Har ila yau, tunanina da addu’o’ina suna zuwa ga wadanda abin ya shafa da iyalansu, cocin Katolika, da gwamnatin jihar Ondo.
“Ba za mu tsorata da son zuciya da abubuwan da ke fakewa a cikin duhu ba. Zamu tsaya tsayin daka wajen yaki da miyagu kuma Najeriya zata yi nasara.
“Kamar yadda shugaban kasa ya yi umarni, hukumomin gaggawa za su tashi tsaye domin kawo dauki ga wadanda suka jikkata.
“Muna tare da jama’ar Owo da Ondo a wannan mummunan lokaci.”
Fatima Abubakar