Yan Bindiga Sun Sace Daliban Jami’a A Zamfara

0
22

 

Da sanyin safiyar yau Juma’a ne aka sace wasu daliban jami’ar tarayya ta Gusau da ba a tantance adadinsu ba a jihar Zamfara.

‘Yan ta’addan masu yawan gaske ne suka mamaye al’ummar Sabon-Gida da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.

Wani mazaunin unguwar Sabon-Gida mai suna Nazeer Sabon-Gida ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar garin ne da misalin karfe uku na safe inda suka fara harbe-harbe ba gaira ba dalili.

 

A cewarsa, an kai hari a dakunan kwanan dalibai uku, kuma ‘yan bindigar sun tafi da dukkan daliban da ke cikin dakunan kwanan dalibai.

“Sun shiga garin da misalin karfe 3 na safe kuma suka fara harbi ba kakkautawa,” in ji shi.

“Har yanzu ba mu tabbatar da adadin daliban da aka yi garkuwa da su ba saboda ‘yan bindigar sun shiga dakunan kwanan dalibai uku tare da yin garkuwa da dukkan daliban da ke wurin,Yana da wahala a iya tantance adadinsu a yanzu.”

Wata majiyar kuma ta ce ‘yan bindigar sun yi artabu da dakarun sojin Najeriya a wani kazamin artabu da ‘yan bindigar amma hakan bai hana ‘yan fashin tserewa da wadanda aka yi garkuwa da su ba.

“Sun dambata sosai da sojojin amma yadda wadannan ‘yan bindigar ke gudanar da ayyukansu, za su raba kansu gida biyu, kungiya daya za ta koma tare da wadanda aka sace yayin da dayan kuma za ta tsaya a baya don kare kungiyar ta farko,” in ji shi.

“Rukunin farko sun tafi tare da daliban yayin da rukuni na biyu suka yi musanyan wuta da sojojin.”

A cikin watan Yuni ne wasu daliban jami’ar suka nuna rashin amincewarsu da yadda aka yi garkuwa da ‘yan makarantarsu a Sabon-Gida da Damba.

Kauyen Sabon-Gida al’umma ce dauke da babban harabar jami’ar tarayya ta Gusau mai tazarar kilomita 20 zuwa babban birnin jihar, Gusau.

Kokarin jin ta bakin mahukuntan makarantar bai yi nasara ba domin mai magana da yawun makarantar Umar Usman bai amsa kiran waya da wakilinmu ya yi masa ba.

Hakazalika, rundunar ‘yan sandan jihar ba ta ce uffan ba game da sabon harin da aka kai.

Firdausi Musa Dantsoho