Yanzu Yanzu: An kashe mutane Biyu, Yayyin da Yan Bindiga da Yan Ta’addan Ansaru A suka samu tangarda

0
116

An samu tashin hankali a karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna yayin da wasu ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan Ansaru suka yi artabu da bindiga.

‘Yan kungiyar Ansaru dai na yin wa’azi ga jama’ar yankin ne a lokacin da ‘yan bindigar suka far wa jama’ar inda suka rika harbe-harbe ba da jimawa ba, inda suka kashe mutanen kauyen biyu.

Lamarin dai kamar yadda aka bayyana wa maneman labarai  cewa ‘yan bindigar sun shiga kauyen Damari da ke karkashin gundumar Kazage da ke yankin Gabashin karamar hukumar da nufin fatattakar ‘yan ta’addan daga kauyen.

An tattaro cewa kungiyar Ansaru ta kwace yankuna da dama a Gabashin karamar hukumar da sunan jagorantar hare-haren ‘yan bindiga.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Shugaban kungiyar BEPU na Masarautar Birnin-Gwari (BEPU), Ishaq Usman Kafai, ya shaidawa manema labarai cewa an dauki tsawon sa’a guda ana rikicin tsakanin kungiyoyin biyu.

A cewarsa, ‘yan kungiyar ta Ansaru wadanda su ma suke  dauke da muggan makamai sun yi galaba a kan ‘yan bindigar wanda hakan ya sanya su (’yan bindiga) suka Kauyen.

Duk da haka, a cewar Kafai, an samu asara da dama yayin arangamar.

“An samu barna a yayin arangamar;  an kona wani shago;  motoci biyu sun kone;  An kona wani Asibiti mai zaman kansa.  ‘Yan bindigar kuma sun kashe wasu mutanen yankin (ma’aikata) guda biyu yayin da ‘yan fashin ke guduwa cikin dajin,” in ji shi.

Ishaq ya shaidawa kafar yada labarai cewa asibitin ya kone bisa kuskure sakamakon gobarar da ta tashi daga wata mota da ta kone.

By: Firdausi Musa Dantsoho