Yanzu-yanzu: Buhari ya bukaci majalisar dattawa ta amince da su biya bashi da ake binsa na $556m, £98,526,013, naira biliyan 226.

0
9

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman majalisar dattawa ta amince da biyan bashin da ake bin sa.

 

An gabatar da bukatar da shugaba Buhari ya gabatar a zaman majalisar na ranar Laraba, inda shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta wasikar ga majalisar.

 

Adadin da ake nema ya kai dala $566,754,584.31, £98,526,012.00, da kuma naira biliyan 226 da gwamnatin tarayya ke bin su.

Buhari ya ba da shawarar bayar da takardun alkawari a matsayin hanyar daidaita wannan bashi.

 

Firdausi Musa Dantsoho