Yarima Harry da matarsa na ziyara a Najeriya.Domin gudanar da Gasar Invictus Games ga Sojojinta

0
18

Yarima Harry ‘Da ne ga Sarki Charles na uku da Gimbiya Diana, ya kasance tsohon soja wanda ya fafata har sau biyu a karo daban-daban a yakin Afghanistan. kuma mutum na biyar cikin jerin masu jiran gadon sarautar masarautar Birtaniya.

Yarima Harry da matarsa, Meghan, sun isa Najeriya a ranar Juma’a, don halartar Gasar Invictus Games, wanda ya kafa don taimakawa wajen farfado da wadanda suka jikkata da marasa lafiya da kuma tsofaffin sojoji, na yankin Afrika ciki har da sojojin Najeriya da ke yaƙi da ‘yan tawaye na tsawon shekaru 14.

Bayan ya bar aikin sojine ya kirkiro da gasar wasannin motsa jiki a matakin kasa da kasa na sojojin da suka sami nakasa a fagen daga mai suna INVICTUS GAMES.

Harry da Meghan za su gana da sojojin da suka jikkata da kuma iyalansu a wani abin da jami’an Nijeriya suka ce na nuna goyon baya ne don inganta yanayi sojojin da jin daɗinsu.

Abidemi Marquis, daraktan wasanni a Hedkwatar Tsaron Najeriya, ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa “Wannan wasannin na Invictus yana bai wa sojojinmu damar murmurewa da dawo da walwalarsu.”
Wannan ziyarar tasu ya burge wasu a Nijeriya, inda ake hasashen zata kyautata dangantaka da gidan Sarautar Birtaniya.

Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana Wasannin Invictus a matsayin wanda zai taimaka wajen karawa tare da warkewar Wani gibi ga dubban jami’anta daga firgicin da suka shiga sakamakon yaƙi da ‘yan kungiyar Boko Haram tun shekarar 2009, lokacin da suka kaddamar da hare-hare.

“Kashi 80 cikin 100 na sojojinmu da suka shiga cikin wannan shirin na farfadowa suna samun sauki (kuma) yanayin rayuwarsu na sauyawa da kyau,” in ji Marquis, daraktan wasanni na soja.

“Shirin farfadowar ya ba su dama don farfaɗo da ƙimarsu, da inganta lafiyar ƙwaƙwalwarsu da hankali.”

 

 

Hafsat Ibrahim