Allah Ya yi wa Hon. Isa Dogon Yaro rasuwa, bayan fama da gajeriya Rashin Lafiya.

0
18

Daga fadar Majalisar wakilai ta kasa, inda ta aikewa manema labarai

Sanarwar Makokin Hon. Isa Dogonyaro, na majalisar wakilai ta 10 a

*Abuja-FCT – Juma’a,

Wanda ya rasu a ranar 10 ga Mayu, 2024* –

 

Majalisar ta ayyana alhinin rasuwar Hon. Isa Dogonyaro (Kogunan Ringim), fitaccen dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Babura/Garki ta jihar Jigawa a majalisar wakilai ta 10.

 

Hon. Dogonyaro ya rasu ne bayan gajeriyar jinya da yayi fama da ita.

 

Dan majalisar mai shekaru 46 a duniya. Ya kasance mai kwazo, da kishin kasa wanda ya yi wa al’ummar mazabarsa da kasa hidima. Ya kasance ginshiki a majalisar, inda ya bayar da gudunmawa sosai wajen samar da dokoki, musamman a fannin yaki da cutar kanjamau, da kuma tarin fuka, harma da fannin yaki da zazzabin cizon sauro, inda ya zama mataimakin shugaban kwamitin a majalisar.

 

Marigayi Wanda ya kasance Dan jam’iyyar All Progressives Congress.

 

Anyi masa shaida wajen

shahara da rikon amana da jajircewa da sadaukar da kai ga rayuwar al’ummar Najeriya Kuma Yana daga cikin zauren masu fafutukar tsabtace majalisar wakilai don ta zama mai tsarki.

 

Hon. Isa Dogonyaro ya kasance dan kishin kasa da aka sani a Fannin kabilanci Kuma shi mai fara’a ga shi da haziki ne. Marigayin yarasu Ya bar mata da ‘ya’ya.

 

Majalisar na Mika taaziyya da addu’o’in su ga iyalansa da mazabarsa da abokan aikinsa, da Kuma al’ummar jihar Jigawa.

 

Za’a gudanar da addu’o’i ga masoyan da suka tashi bayan sallar Juma’a a yau, da karfe 2:30 na rana a babban masallacin kasa dake Abuja, inda kuma za’a gudanar da addu’a kamar yadda addinin musulunci ya tanada a makabartar Gudu Muslim.

 

Allah ya jikansa da rahma, Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma saka masa da Al-Janat Firdausi.

 

Sa hannu,

 

*Rep Akin Rotimi, Jr.*

Kakakin Gidan

Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a.

 

 

 

 

Hafsat Ibrahim.