0
160

Wani babban abokin ango a unguwar Gaida da ke karamar hukumar Kumbotso a jahar Kano ya sace kayan aure na amaryar da kudinsu ya kai kimanin dubu dari biyar.

Lamarin dai ya faru ne bayan mako guda da daurin auren yayin da wanda ake zargin ke rike da makullin gidan ma’auratan.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, kwamandan ‘yan banga na Gaida, Shekarau Ali, ya ce angon ya kai rahoton lamarin kuma sun kama wanda ake zargin bayan gudanar da bincike.

A cewarsa, wanda ake zargin ya samu makullin ne daga hannun ‘yan uwan ​​amaryar tare da cewa zai mika su ga ango.

Ya ci gaba da cewa, “Angon ya nemi a mayar masa makullin amma ya ki. Da ya ga ma’auratan sun fita daga gidan, sai ya bude gidan ya sace akwatunan aure da kayan abinci.”

Ya kara da cewa suna kan bincike akan lamarin  kuma za su mika shi ga hukumar ‘yan sanda.

A halin da ake ciki, wanda ake zargin ya amince da aikata laifin, inda ya ce shaidan ne ya sa shi ya ci amanar abokinsa kuma ya roki gafarar sa.

Sai dai wanda ake zargin ya ce ya bayar da gudunmawa wajen daurin auren ne ta hanyar kashe sama da Naira 400,000 ga angon.

Daga Fatima Abubakar