CHINESE CHICKEN FRIED RICE

0
703

 

Abubuwan Bukata Wajan Hada Chinese Chicken Fried Rice:

 

*Shinkafa 3 cups

*Man gyada 6 tbsp

*Karas 2

*Peas 1/6 cup

*Tattasai 2

*Koren tattasai 2

*kaza 1

*Kwai 2

*Soy sauce 1/6 Cup

*Sinadarin Dandano

Yadda Ake Haddawa

  1. zaki tafasa shinkafan ki, saiki wanke ki cire starch din.
  2. Sai ki yayyanka  su karas, kaza, tattasai, ki aje su a gefe.
  3. Kisa man gyada da albasa a wuta, in ya soyu ki sa soy sauce cokali biyu da kazar ki da kika yanyanka kika tafasa saiki soya shi na minti biyar.
  4. saiki zuba tattasai, peas da duk sauran abubuwan da kika yanka ki kara soyasu na minti biyar. Sai ki xuba shinkafar kita jujjuyawa sai ki zuba ruwan tafashen kazar kadan ki rufe har tayi.
  5. Sai kiyi scrambled egg ki zuba akan shinkafar ki saiki zuba sauran soy sauce din da dan maggi kadan yadda zai zaiji a shinkafan ki sai ki rufe ya karasa.
  6. Toh Chinese chicken fried rice ya haddu aci da duminsa.

 

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho