YADDA  AKE HADA GUGGURU (POPCORN)

0
1746

 

ABUBUWAN BUKATA SUNE:

* Masarar gugguru(jah)

* sugar

* butter

* madara

 

YADDA AKE HADAWA

 

  1. Zaki wanke masararki saiki barta ta bushe akwai kuma wacce ake siyarwa a stores mai kyau ba saikin wanke ba.
  2. saiki samu frying pan dinki ko tukunya ki zuba butter da sugar ki kunna wuta kadan yana narkewa zaki iya diga kowani irin flavour domin kamshi idan kina so.                                   
  3. ki juya  hadin siganki da butter saiki zuba wannan masarar taki ki juya sosai saiki rufe na minti biyar(5)minute.
  4. Bayan minti biyar zakiga ya fara komawa gugguru yana tsalle shiyasa akeso a rufe tukunyar da zaran an saka masarar.   
  5. Bayan kin rufe saiki dinga dubawa sabida karya kone.
  6. In ya gama haduwa saiki samu roba mai kyau ki juye saiki dauko madara ki barba kina juyawa shikkenan guggurun ki ya hadu.

 

 

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho