Abinci biyar 5 da Ke zuke sukari a jikin mu 

0
275
Photo taken in Dhaka, Bangladesh

 

 

Nau’in abincin da muke ci koyaushe yana da tasiri mai zurfi akan lafiyar mu na yau da kullum , ko dai mai kyau ko mara kyau. An danganta yawan cin abinci mai sukari da yanayin kiwon lafiya da yawa da suka haɗa da kiba da nau’in ciwon sukari na 2. Yawan cin waɗannan abinci da abubuwan sha masu sukari, Abu ne da ba a  iya kaurace masa  kuma iya abun da mutum zai iya yi shine daidaita yawan cin su.

 

Idan aka yi la’akari da yawan ƙalubalen kiwon lafiya da ke da alaƙa da shan sukari da kuma matsalolin da ke tattare da shi, ba zai zama mummunan ra’ayi ba idan mun ƙara yawan abincin  da aka sani don zube sukarin da Ke cikin abincin da mu Ke ci kuma yana rage sakin sukari cikin jinin mu. Wannan zai taimaka sosai wajen rage haɗarin cututtuka da yawa da ke da alaƙa da yawan shan sukari, musamman ma ciwon sukari.

Kadan daga cikin ƴan misalan irin waɗannan abincin sune:

 

  1. Wake da lentil

Wake da lentil suna daya daga cikin abinci masu gina jiki saboda sinadarai masu gina jiki wanda ya ƙunsa irinsu fiber, magnesium, da furotin waɗanda aka sani suna da tasirin rage sukarin jini. Kasancewa su da fiber Mai yawa da rashin daukan sitaci shima yana taimakawa wajan narkar da abinci a hankali da kuma yana taimakawa haɓaka jikin mu wajan amsawar sukari  bayan cin abinci.

 

  1. Kale

Kale ana ɗaukarsa a matsayin  abinci Mai inganci ne saboda wadataccen sinadaran sa wanda ya haɗa da fiber da flavonoid antioxidants waɗanda ke taimakawa wajan rage yawan sukari na jini ta hanyar zuka sukari mai yawa a cikin abincin . Flavonoid antioxidants da ake samu a kale kamar quercetin da kaempferol suma suna da tasirin wajan rage yawan sukari.

 

  1. Berries

Irin su blackberry, rasberi, da strawberry suna da wadatan  fiber, minerals, na antioxidant a cikinsu. Duk waɗannan sinadiran da berries suka kunsa ya sa ya zama kyakkyawan abinci da Ke haɓaka daidaituwan sukarin a jini. Cin su yana da alaƙa da raguwar insulin bayan cin abinci da matakan sukari na jini, kuma suna taimakawa wajen haɓaka insulin da kuma cire glucose daga jini.

 

  1. kubewa

 

Okra ‘ya’yan itace ne mai lafiya kuma baya ga kasancewa da sinadirai masu ban sha’awa, kuma yana da wadataccen sinadarai masu rage 

sukari kamar su polysaccharides da flavonoid antioxidants. Rhamnogalacturonan yana da tasirin anti-diabetic, isoquercitrin da quercetin 3-O-gentiobioside kuma suna da kaddarorin anti-diabetic waɗanda ke taimakawa hana wasu enzymes waɗanda zasu iya haɓaka sukarin jini.

 

  1. Tuffa

Tuffa na ɗaya daga cikin ‘ya’yan itatuwa masu yawan sinadaran gina jiki kuma suna dauke da sinadirai irin su fiber da kwayoyin shuki irin su quercetin, chlorogenic acid, da gallic acid. Duk waɗannan sinadirai suna da alaƙa wajan rage sukarin jini da kariya daga ciwon sukari da kuma cin su kafin cin abinci yana da alaƙa da raguwar sukarin jini bayan cin abinci.

By: Firdausi Musa Dantsoho