Yadda Ake hada Miyan Taushe Mai Dadi.

0
1644

 

 Kuna da bukukuwa da kuke ɗaukin yi? Kuna da wani biki da kuka rasa wanni irin  miya zaku dafa? Idan eh, ya kamata ku gwada Miyan Taushe kuma za ku yi farin ciki da yin hakan. Miyan Taushe abinci ne na Arewacin Kasar Najeriya kuma Hausawa da Fulani ne ke cin sa. Miya ce da ake hadda wa da  kabewa (pumpkin) kuma galibi ana cin sa  lokutan bukukuwa, amma wasu suna ɗaukar sa a matsayin abinci na asali (kamar don abincin rana ko abincin dare). A cikin wannan girke-girken namu na yau, zan koya muku yadda ake hadda Miyan Taushe.

Miyan Taushe yana da sauƙin dafa wa, ga daɗi sosai, kuma yana da sinadarai masu gina jiki. Ku bi ni yayin da nake ɗaukar ku ta hanyar matakan  yadda ake hadda shi.                     

Abubuwan bukata don hada Miyan Taushe

Kuna buƙatar abubuwan da ke gaba don yin Miyan Taushe:

*kabewa (pumpkin) guda daya

* kofi daya na man ja ko man gyada

*½ kofin gyada (nikkaken gyada)

*Nikkaken  tumatir

*Nikkaken Barkono 

*Alayyahu yankakken 

*Albasa niƙkake

*Kayan kamshi da dandano kamar thyme, curry, maggi, da gishiri.

*Kifi ko nama

*Kofuna 3 na ruwa

Yadda ake hadda miyan taushen

 1. A dora tukunya mai tsafta a wuta sannan a zuba man ja ko man gyada.
 2. A Yanka albasa a saka a cikin tukunyan.
 3. A bar albasan ta soyu na tsawon mintuna 3 zuwa 5 a ƙarƙashin matsakaicin zafi har sai ta zama launin ruwan kasa.
 4. A zuba  niƙkaken  tumatir, barkono, da albasa. Sai a soya na minti 10.
 5. A yanka kabewan a zuba a tukunyar ya dafu.
 6. A Ƙara kofuna 2 na ruwa a tukunyar dafa miyan  kuma.
 7. Sai a sa kifi ko nama a cikin tukunyar dafa miyan sai a bashi  damar dafuwa na mintina 20.
 8. Sai ki Yanka ƙarin albasa ki ajiye su a gefe tare da yankakken alayyahun ki.
 9. Ki sa gyadan ki  niƙkake a cikin tukunyar miyan ki sai a dafa na mintuna 5 zuwa 8.
 10. Sai a sa  kayan ƙamshi da dandano(maggi, curry, gishiri, da dai sauransu) sai a kuma motsa miyan da kyau. A Ba sa minti 10 ya dafu.
 11. Ku ɗanɗana domin tabbatar da komai ya daidaita   idan akwai buƙatan kari sai a kara.
 12. A Rage zafin wutan sai a zuba albasa da yankakken alayyahu a ba shi damar ya turara  na mintuna 10 zuwa 15.
 13. Shi kenan Miyan Taushen ku ya haddu.     

 A gargajiyance, galibi ana cin Miyan Taushe da Tuwon Masara, Tuwon Shinkafa, Tuwon Alkama,  Tuwon Dawa, masa da sinasir.

 

By: Firdausi Musa Dantsoho