A lahadin da ya gabata ,ashirin ga watan maris(20-03-2022).ne aka samu karuwa a fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Hanaan ‘ya ce ga shugaba Buhari da uwargidan sa Aisha Buhari wacce aka aurar da ita a watan satumban 2020 ga angon ta Muhammad Turad.
Wata majiya da ke kusa da iyalan Shugaban, sun sanar mana da cewa, Hanaan ta haifi da na miji a lahadin da ya gabata a kasar Turkiya.
Inda aka ce da Uwa ,Uba da kuma baby suna cikin koshin lafiya.Allah Ya raya abinda aka samu.
By Fatima Abubakar.