BABBAN TARON KUNGIYAR YADA LABARAI TA NAJERIYA KARO NA 76.

0
40

A yau ne 22 ga watan maris 2022,kungiyar yada labarai ta Najeriya ke gudanar da babban taron ta karo na 76 a Abuja.

Taron wanda Multichoice suka shirya da hadin gwiwar Broadcasting Organisation of Nigeria (BON)da kuma Broadcast Media Africa.

Taron dai an shirya shi domin fadakarwa ,ilmantarwa da kuma wayar da kan manema labarai wurin gudanar da ayyukan su cikin kwarewa da zamani.

Taron ya samu wakilcin manya -manyan baki daga gida da waje.wanda suka hada da shugaban Ghana Broadcasting Corporation Amin Alhasan,Tony Akiotu shugaban AIT,Tunde Akinlolo shugaban kungiyar tsara fina-finally,Malam Balarabe Illela shugaban. NBC,da wanda ya gabatar John Ugbe ciyaman na BON kuma CEO/MD Multichoice Nigeria.

Da yake jawabin bude taro,ministan yada labarai Alh.Dr Lai Muhammad, wanda Mr Ayo Adewunyi ya wakilta, ya gargadi yan jarida da su dinga tantance labaran karya da gaskiya kafin su yada,kuma ya yi Jan kunne ga biye wa labarai marasa kan gado,a wannan yana yi na siyasa.Yayi wa kowa fatan alheri yayin ci gaban taron.

By Fatima Abubakar