HANAAN BUHARI TA HAIFI DA NAMIJI A KASAR TURKIYA.

0
202

A lahadin da ya gabata ,ashirin ga watan maris(20-03-2022).ne aka samu karuwa a fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Hanaan ‘ya ce ga shugaba Buhari da uwargidan sa Aisha Buhari wacce aka aurar da ita a watan satumban 2020 ga angon ta Muhammad Turad.

Wata majiya da ke kusa da iyalan Shugaban, sun sanar mana da cewa, Hanaan ta haifi da na miji a lahadin da ya gabata a  kasar Turkiya.

Inda aka ce  da Uwa ,Uba da kuma baby suna cikin koshin lafiya.Allah Ya raya abinda aka samu.

By Fatima Abubakar.