An sako mutane 11 daga cikin wayanda aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

0
122

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Asabar din da ta gabata ne ‘yan ta’addan suka sako mutanen da suka sace daga Kaduna zuwa Abuja maza biyar da mata shida

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’adda ne, a ranar 28 ga watan Maris, 2022, sun yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja, bayan sun kashe fasinjoji tara, tare da raunata wasu.

An sako wadanda harin ya rutsa da su 11 a ranar Asabar, bayan cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya.

‘Yan ta’addan dai sun yi barazanar fara kashe wadanda abin ya shafa matukar Gwamnatin Tarayya ta ki tattaunawa da su.

Mawallafin Desert Herald, Tukur Mamu, wanda ya kasance mai shiga tsakani, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce majiyar sa ta shaida masa cewa ‘yan ta’addan sun sako mutanen da aka yi garkuwa da su bisa la’akari da lafiyarsu, inda ya ce matan na daga cikin wadanda ake garkuwa da su.

“Da farko dai ana sa ran za a sako dukkan matan da aka sace a kashin farko yayin da za a ci gaba da tattaunawa don ganin an sako sauran wadanda aka sace amma wadanda suka yi garkuwa da su sun yanke adadin matan da suka amince a sako tun farko, saboda gwamnatin Najeriya ta bukaci hakan. wadanda aka saki sun hada da watanda ke cikin wani hali a bisa rashin lafiya inji shi.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a tabbatar da sunayen wadanda aka saki

Daga Fatima Abubakar