Aisha Buhari ta bukaci a tallafa wa Ilimin yara marasa galihu

0
57

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bukaci masu ruwa da tsaki da su tallafa wajen bunkasa ilimi da tattalin arzikin yara marasa galihu a kasar nan.
Aisha ta bayyana haka ne a ranar Asabar yayin kaddamar da gidauniyar MA’ARUF da kuma tara kudade da uwargidan gwamnan Yobe, Misis Hafsat Kollere-Buni ta kafa a Abuja.

Uwargidan shugaban kasa wadda ta samu wakilcin uwargidan shugaban hafsan sojin kasa, Mrs Salamatu Yahaya, ta nuna jajircewa da kuma kishin wanda ya kafa wajen tallafawa masu karamin karfi a jihar Yobe.
“Hakika na yi matukar farin ciki da ganin muna da matar shugaban kasa mai kishin rayuwar mata da yara.

Haƙiƙa, ƙudurin gidauniyar MA’ARUF na ƙaddamar da ayyuka a fannonin ilimi, ƙarfin tattalin arziki da samar da ayyukan kiwon lafiya zai ƙara taimakawa ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya.
“hakazalika gidauniyata ta Future Assured Foundation tana kokarin samar da ayyukan jin kai da ake bukata ga al’ummar Najeriya,” in ji ta.

Don haka Aisha Buhari ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su hada karfi da karfe su marawa gidauniyar baya domin tallafawa mata da yaran Yobe.”Ina kuma so in yi kira ga duk mutanen da ke nan da su taimaka wa wannan gidauniya,” in ji ta.

Uwargidan shugaban kasar ta tunatar da taron irin gagarumin ci gaban da gidauniyarta ta samu a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.
A cewarta, Gidauniyar Future Assured ta yi tasiri sosai a fannonin aikin yi, kiwon lafiya da kyautata rayuwar mata da yara ta hanyar bayar da shawarwari.

“The Future Assured ya yi aiki sosai a cikin shekaru shida da suka gabata kuma ya taimaka wa iyayen yaran makarantar Buni Yadi wadanda su ne ‘yan kunar bakin wake da sauransu,” in ji ta.

Don haka ta taya wanda ya kirkiro wannan shiri mai ban sha’awa kuma ta bukace ta da ta ci gaba da yin aiki.

Daga Faiza A.gabdo