Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Mr. Festus Keyamo ya ce sunan mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo baya cikin jerin kwamitin yakin neman zabe saboda umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar.
Keyamo, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce Buhari ya bayar da umarnin cewa a cire sunayen Osinbajo da sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Mr Boss Mustapha domin ba su damar maida hankali kan harkokin mulki.
Ya ce dukkan muhimman ayyukan gwamnati ba za su iya barin mukamansu don yakin neman zabe ba.
Kakakin ya jaddada cewa jam’iyyar APC mai mulki tana da hakkin al’ummar Najeriya na gudanar da mulkin kasar a madadinsu a kalla har zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2023, kuma jam’iyyar na da niyyar yin hakan ne da dukkan alamu.
Ya ce: “An jawo hankalinmu ga wasu labaran da ke ta yawo cewa za a iya samun matsala a cikin gidan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) saboda sunan mataimakin shugaban kasa mai daraja, Farfesa Yemi Osinbajo, SAN. , GCON, baya cikin jerin sunayen Tinubu/Shettima Presidential Campaign Council.
“Babu wani abu da zai yi nisa daga gaskiyar. Domin kaucewa shakku, shugaban kasa Muhammadu Buhari GCFR, shine shugaban kwamitin yakin neman zaben. A sakamakon haka, Shugaban ya bayar da umarnin musamman cewa a cire mataimakin shugaban kasa da sakataren gwamnatin tarayya, Mr. Boss Mustapha a cikin Majalisar Yakin Neman Zabe domin mayar da hankali kan tafiyar da mulkin kasa da gudanar da mulki.
“A matsayinsu na yan jam’iyya da gwamnati da ke da alhaki, duk muhimman ayyukan gwamnati ba za su iya barin mukamansu don yakin neman zabe ba. Jam’iyyar APC tana da hakkin al’ummar Najeriya na gudanar da mulkin kasar a madadinsu akalla har zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2023, kuma muna da niyyar yin hakan ne da dukkan wani nauyi da ya rataya a wuyanmu.
“Ba za mu bi tafarkin wadanda suka gudanar da mulkin kasar nan a gabanmu ba kuma jam’iyyarmu ba ta cikin rudani kamar wadanda ke son ceto kasar, amma ba za su iya tafiyar da harkokinsu na cikin gida ba.”
Daga Faiza A.gabdo