‘Yan Bindiga Sun Sace Alƙalin Babbar Kotun Kebbi, Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza

0
41

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza, bayan sun kai hari gidansa da ke garin Bunza a daren Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na dare, jim kaɗan bayan Mai Shari’ar ya dawo gida daga wata tafiya da ya yi zuwa Jihar Sokoto.

Shaidu sun ce maharan sun kutsa cikin gidan tare da yin awon gaba da alkalin zuwa wani wuri da ba a sani ba. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana ko sun tuntubi iyalansa ko kuma sun nemi kuɗin fansa ba.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an tsaro sun fara bincike tare da ƙaddamar da wani samame domin ceto Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza da kuma kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Lamarin ya jefa al’ummar garin Bunza da ma daukacin Jihar Kebbi cikin fargaba, yayin da ake kira ga jami’an tsaro su gaggauta ɗaukar matakan da za su tabbatar da kubutar da alkalin cikin ƙoshin lafiya tare da hukunta masu hannu a wannan aika-aika

To sai dai wasi rahotanni sun bayyana cewa an sace alkalin ne da sanyin safiyar Lahadi a gidansa da ke kan titin Zogirma, a Karamar Hukumar Bunza ta Jihar Kebbi.

Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:00 na tsakar dare, jim kadan bayan alkalin ya dawo daga wata tafiya zuwa Jihar Sakkwato.

An ce bai dade da dawowa ba sai wasu dauke da makamai suka mamaye gidansa suka yi awon gaba da shi.

Wata majiya ta ce, duk da cewa ba a ji wa kowa a gidan rauni ba, maharan sun rika harbe-harbe kafin su tafi da alkalin.

Majiyar ta kara da cewa nan take aka sanar da hukumomin da abin ya shafa, ciki har da shugabannin Babbar Kotun Jihar.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, “Zan iya tabbatar da cewa Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza an yi garkuwa da shi daga gidansa da ke Bunza da misalin tsakar dare.”

Ya kuma bayyana cewa, bayan samun rahoton sace alkalin, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, CP Umar Muhammad Hadejia, ya gaggauta tura jami’an rundunar musamman da na tattara bayanan sirri domin tabbatar da ceto shi cikin koshin lafiya.

A cewarsa, “A halin yanzu jami’anmu na ci gaba da sintiri da bincike a wuraren da aka gano, ciki har da dazuka, domin ceto alkalin ba tare da ya samu wata illa ba.”

Wani babban jami’in Babbar Kotun Jihar Kebbi, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai bayyana shi a matsayin abin takaici ga bangaren shari’a.

Ya ce, “Ba ni da izinin yin bayani a hukumance, amma wannan lamari abin takaici ne matuka. Jin cewa an yi garkuwa da daya daga cikin alkalanmu daga gidansa abin damuwa ne sosai.”

Ya kara da cewa mahukuntan Babbar Kotun sun riga sun gana da shugabannin hukumomin tsaro na jihar domin tsara hanyoyin tabbatar da kubutar da alkalin cikin gaggawa.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata kungiya da ta dauki alhakin sace Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza.

 

 

Hafsat Ibrahim