Fidda Gwani Na APC a Wata Jiha, kotu Ta Yi Fatali da Wadanda Suka Ci Zabe

0
39

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Port Harcourt ta soke zaben fidda gwanin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ribas.
kotun ta zartar da hukuncin ne a jiya Litinin yayin sauraron wata kara da wasu fusatattun mambobin APCn suka shigar a gabanta.
Idan za a tuna, fusatattun mambobin sun yi zargin cewa an ware su a yayin zaben fidda gwanin jam’iyyar inda suka yi zanga-zanga sakatariyarta da ke Port Harcourt.
Sai dai kuma, wani mai suna George Orlu da wasu mutane hudu da suka yi ikirarin siyan fam din takara sun tunkari kotu inda suka bukaci a soke zaben fidda gwanin APC a jihar.
Da take yanke hukunci, kotun ta bayyana cewa an tsame mutanen daga zaben fidda gwanin ba bisa ka’ida ba. Justis E.A. Obile, a hukuncinsa, ya riki cewa an fitar da fusatattun mutanen daga zaben fidda gwanin ba bisa doka ba, yana mai cewa hakan yasa aka soke shi.
Obile ya yarda da masu karar cewa an tsame su a tsarin shiga zaben fidda gwanin jam’iyyar ba bisa ka’ida ba. Don haka ya yanke hukunci cewa an soke zaben kuma kada a dauki wadanda aka zaba a tsarin a matsayin yan takara.
Daga Faiza A.gabdo