Mutane 5 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Kaduna

0
9

Akalla fasinjoji biyar ne suka rasa rayukansu a kan hanyar Kaduna zuwa Kachia a lokacin da motar bas din da suke tafiya a ciki birki ya tsinke mata.
A cewar Mista Joseph Amos, daya daga cikin fasinjojin da suka tsira, wanda a halin yanzu suke karbar magani a wani asibiti, a Kaduna, “mun hau motar bas din daga Kaduna zuwa Kafachan. Mu takwas ne a cikin bas din, ba zato ba tsammani, bas din ta kwace kuma ta bugi gefen hanya.

Mutane biyar ne suka mutu nan take.”
Ya ce lokacin da direban ban din ke gudun wuce kima, sun gargade shi a kan hanya babu kyau ga kuma ramuka, amma bai saurare su ba.
An kai wadanda suka mutu zuwa dakin ajiyar gawa da ke wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.
Kwamandan sashen hukumar kiyaye hadura ta tarayya da ke Kaduna, bai amsa kiran wayar da aka masa ba don tabbatar da faruwar lamarin zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Daga Faiza A.gabdo