Tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, kuma daya daga cikin masu neman takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Adamawa, Nuhu Ribadu, ya janye aniyar kalubalantar nasarar Aisha Binani a kotun koli.
Mista Ribadu, wanda ya zo na biyu a zaben fidda gwani, ya kalubalanci nasarar Misis Binani kan zargin sayen kuri’u, da jerin sunayen wakilai ba bisa ka’ida ba, a zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar 27 ga watan Mayu.
A ranar 24 ga watan Nuwamba, wata kotun daukaka kara da ke zamanta a Yola ta yi watsi da hukuncin wata babbar kotun tarayya, wadda ta soke zaben fidda gwani na jam’iyyar APC amma ta bayyana cewa jam’iyyar ba ta da dan takara.
A wata wasika mai dauke da kwanan 2 ga watan Disamba, kuma aka mika wa mukaddashin shugaban jam’iyyar APC na jihar Adamawa, Mista Ribadu, ya ce duk da cewa yana da hakki kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, amma ba shi da niyyar cigaba da karar.
Wasikar tana cewa: “Kamar yadda kuka sani, Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan takaddamar da ta taso daga zaben fidda gwanin gwamnonin mu, wanda ya sabawa fatan da muka yi a karar da na kafa.
“Tun daga lokacin nake tuntubar iyalai na, abokan siyasa, da shugabannin jam’iyya a matakai daban-daban kan mataki na gaba.
“Bugu da kari, na yi tunani sosai kan manufa ta na siyasa, musamman burina na zama gwamnan Adamawa.
“Dalilin da ya sa na yi burin yin mulki a jihar shi ne don samun damar yi wa jihar hidima a matsayin gudunmawar da zan ba jihar nan gaba. Wannan aiki ne da aka fara da abokan arziki wadanda suka sa ni yarda da cewa ina da kwarewa da kuma abin da zai iya taimakawa wajen ci gaban jiharmu.
“Ina so in yi amfani da wannan damar in gode wa masu fatan alheri da kuma dumbin magoya bayana wadanda suka sadaukar da kansu da kuma bayar da goyon baya ga gagarumin fatan alheri da goyon bayan da na samu daga gare su tsawon shekaru.
“Wannan shi ne yunkurina na biyu na karbar tikitin jam’iyyarmu. A 2019 na bayar da kaina amma na rasa damar zama dan takarar jam’iyyata. Sai dai kuma a rubuce yake cewa don nuna kyakykyawar dabi’ar da kuma kare muradun jam’iyyata ta APC, na janye kuma marawa wanda ke rike da tikitin takara kuma na goyi bayansa har zuwa karshe.
“Na yanke shawarar bin haki na a wannan karon, bisa wannan dalili. A karshen zaben fidda gwani na gwamna, wanda aka gudanar a ranar 26 ga Mayu, 2022, wakilanmu sun ba da rahoton kararrakin karya doka da rashin bin ka’ida. Rahotannin ‘yan sanda da na INEC da kuma kwamitin daukaka kara na jam’iyyar sun tabbatar da haka, amma babu wani bayani da ya fito daga cikin gida.
“A saboda haka ne muka garzaya kotu domin neman adalci. Babban Kotun Tarayya ta amince da mu, amma ta yanke shawarar cewa jam’iyyar ba ta da dan takara, wanda ba abin da muka yi fata ba ne. A hukuncin da ta yanke, Kotun daukaka kara, ta mayar da dan takarar da aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani. Bamu yarda da hukuncin ba amma ba ni da niyyar jan wannan ko kadan.
“Na yanke shawarar barin halin da ake ciki ya ci gaba da kasancewa don amfanin jam’iyyar da hadin kan ta.
“A matsayina na dan jam’iyya na gaskiya, ina kira ga dukkan magoya bayana da kada su yanke kauna amma mu ci gaba da rike amanar jam’iyyarmu. Kada mu bari duk wani koma-baya ya shafi kishi da goyon bayanmu ga babbar jam’iyyarmu. Ina kira ga dukkan magoya bayana da su goyi bayan duk ‘yan takararmu.
“Ina kuma mika godiya ta musamman ga shugabannin jam’iyyar na jiha a karkashin jagorancin ku bisa goyon baya da karfafa gwiwa, kuma ina kira gare ku da ku ci gaba da jajircewa wajen yi wa jam’iyyarmu hidima.
Daga:Firdausi Musa Dantsoho