Abbas Ya Zama Shugaban Majalisar Wakilai

0
46

TAJUDDEEN Abbas, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, ya zama shugaban majalisar wakilai a wata kuri’ar da aka kada ranar Talata a harabar majalisar dokokin tarayya da ke Abuja.

Ya doke takwaransa na APC Aminu Jaji da Ahmed Idris Wase.

Abbas ya samu kuri’u 353 daga jimillar kuri’u 359, yayin da Wase ya samu kuri’u 3, Jaji kuma ya samu kuri’u uku.

A halin yanzu Abbas ya kasance wakilin tarayya mai wakiltar mazabar Zaria a majalisar wakilai ta tara.

Abbas, wanda ya kasance dan majalisar tun a shekarar 2011, daga nan ne aka rantsar da shi a matsayin sabon kakakin majalisar wakilai wanda ya gaji Hon Femi Gbajabiamila wanda yanzu shi ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Bola Tinubu.