Tinubu Ya Nada Ribadu, Alake da Wasu Mutane Shida A Matsayin Masu Bashi Shawara Na Musamman

0
29

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin mutane takwas a matsayin masu ba shi shawara na musamman.

Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na fadar gwamnatin Abiodun Oladunjoye ya fitar a ranar Alhamis.

SOLACEBASE ta ruwaito cewa wadanda aka nada sun hada da Mista Dele Alake, mai ba da shawara na musamman kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, Mista Yau Darazo, mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa da gwamnatoci, Mista Wale Edun, mai ba da shawara na musamman kan harkokin kudi da Mrs. Olu Verheijen Mashawarciya na Musamman kan Makamashi.

Sauran sun hada da Mista Zachaeus Adedeji, mai ba da shawara na musamman kan harkokin kudaden shiga, Mista Nuhu Ribadu, mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro, Mista John Ugochukwu Uwajumogu, mai ba da shawara na musamman kan harkokin masana’antu, kasuwanci da zuba jari da Dr (Mrs.) Salma Ibrahim Anas, mai ba da shawara ta musamman.

Firdausi Musa Dantsoho