Wike ya ci alwashin yin garambawul domin tabbatar da gaskiya wurin aiwatar da ayyuka.

0
36

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya bayyana a matsayin abin kunya matuka game da sauye-sauyen kwangilolin da ya yi ta fama da su tun bayan da ya fara aiki domin ganin an  kammala aikin da aka yi watsi da shi.

Ministan wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis din ta yau yayin ziyarar gani da ido a madatsar ruwa ta Usuma, a Bwari, ya kara da cewa bambamcin kudaden da aka samu a cikin kwangilolin ba kawai abin tsoro bane, amma kuma ba za a amince da shi ba.

Wike ya tambayi dalilin da yasa kwangilar tsarin ruwa ta Usuma wanda aka bayar a matsayin aikin gaggawa a shekarar 2017 akan kudi N20b, kuma aka kara gyara har zuwa N50b a shekarar 2020, duk da haka rahoton dan kwangilar ya ce za a bukaci sama da N900m domin kammala aikin duk da cewa sun kai kashi casa’in cikin dari.

Ya lura cewa gwamnatinsa ba za ta amince da irin wannan bambancin ba domin ya sha alwashin yin garambawul ga daukacin al’umma domin tabbatar da gaskiya wajen bayar da kwangila da aiwatar da ayyukan.

 

Daga Fatima Abubakar.