Shari’ar Sheikh Abduljabbar: Kotu Ta Kori batun Ɗaukaka Ƙara, Inda ta Mayar Da Maganar Gaban Babban Alƙalin Jihar Kano (Chief Judge
Daga Ghaddafi Isyaku Muhammad
Babbar Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Kano, ƙarƙashin jagorancin alƙalai uku, Mai shari’a Mohammed Lawal-Shuaibu, tare da Mai shari’a Abubakar Mu’azu-Lamido da kuma Mai shari’a Ahmad Ramat-Mohammed, ta umarci a mayar da shari’ar Malam Abduljabbar Nasiru Kabara gaban Babban Alƙalin Jihar Kano (Chief Judge) domin sake duba ta bisa ƙa’ida, bayan gano kura-kurai a takardun da aka shigar.
A zaman kotun na ranar Alhamis,
an tafka muhawara mai zafi tsakanin malamin, wanda ya bayyana cewa zai kare kansa da kansa, da kuma lauyoyin gwamnati.
Malam Abduljabbar ya roƙi kotun da kada a mayar da shi gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja, inda ya yi zargin cewa rayuwarsa tana cikin haɗari a can.
Haka kuma, malamin ya nuna shakku kan takardun da aka kai masa gidan yari, inda ya zargi cewa lauya ne ya kai masa maimakon ɗan aiken kotu.
Sai dai kotun ta tabbatar masa da cewa wanda ya kai takardar ɗan aikenta ne na halal, ba lauya ba.
Lauyoyin Gwamnatin Jihar Kano, Barista Bashir Sale da Barista I.A. Garba, sun buƙaci kotun da ta kori ɗaukaka ƙarar malamin baki ɗaya.
Sun hujjatar da cewa an shigar da ƙarar ne ba tare da bin ƙa’idojin shari’a ba, don haka babu dalilin ci gaba da sauraron ta.
Ita ma kotun, bayan bincike, ta amince cewa takardun da duka ɓangarorin biyu suka shigar ba su tafi daidai da tanadin doka ba.
Kotun ta tunatar da Malam Abduljabbar cewa wannan kotu ce ta ɗaukaka ƙara, ba kotun da aka yi masa shari’a a baya ba. Alƙalan sun bayyana cewa Har yanzu akwai sauran shari’a a gaban kotun ƙasa wadda ba a sanya ranar ci gaba da ita ba.
Sannan Akwai bayanan cewa wani lauya, Barista Adamu Abubakar, ya riga ya shigar da ƙara a madadin malamin a kotun ƙasa.
Kotun ta nanata wa malamin cewa doka ta ba shi damar neman lauya, kuma idan ba shi da hali, gwamnati tana da nauyin samar masa da lauyan da zai kare shi saboda nauyin shari’ar.
Bayan duka ɓangarorin biyu sun amince cewa a koma kotun ƙasa domin yin gyara, kotun ɗaukaka ƙarar ta yanke shawarar mayar da maganar gaban Babban Alƙalin Jihar Kano.
Kotun ta bayyana cewa tun da babu wani takamaiman hukunci da aka riga aka yanke a yanzu, kuma takardun kowa na ɗauke da kuskure, gara a bi hanyar da doka ta tanada domin yi wa kowa adalci.
Wannan mataki ya kawo ƙarshen zaman na yau, yayin da ake jiran mataki na gaba daga ofishin Babban Alƙalin Jihar.
Hafsat Ibrahim kawo



