Yan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan jihar Benue

0
21

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da kwamishinan yada labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar BENUE, Matthew Abo.

An sace Abo ne daga gidansa da ke mahaifarsa a unguwar Zaki-Biam a karamar hukumar Ukum a ranar Lahadi da daddare.

An rantsar da wanda aka yi garkuwa da a matsayin mamba a majalisar zartarwa ta jihar Benue a ranar 29 ga Agusta, 2023.

Ya fito ne daga karamar hukumar Ukum wadda ta kasance babbar matattarar miyagun ayyuka.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce wasu ‘yan bindiga ne suka yi awon gaba da kwamishinan a kan babura hudu daga gidansa da ke Zaki-Biam, gari da ya shahara da kasancewar kasuwar doya mafi girma a kasar.

A nasa labarin, Tahav Agerzua, tsohon mai taimaka wa tsofaffin gwamnonin jihar biyu kan harkokin yada labarai, ya rubuta cewa a lokacin da ‘yan bindigar suka isa gidan kwamishinan yada labaran, sun umarci kowa da kowa, ciki har da matarsa ​​da ‘ya’yansa da su kwanta. inda suka dauke shi zuwa wani wurin da ba a san inda suke ba akan daya daga cikin baburan.

Ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun tilasta wa kwamishinan da makami ya zauna a bayan daya daga cikin baburan yayin da wani dan bindiga ya zauna a bayan shi.

An kuma tattaro cewa an kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.

Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene, har yanzu ba ta amsa sakon tes da aka aika mata ta wayar tarho domin tabbatar da faruwar lamarin ba.

Sai dai Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar, Hyacinth Alia, Kula Tersoo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, “Abin takaici, an yi garkuwa da shi (kwamishina) a gidansa da ke karamar hukumar Ukum, da misalin karfe 8 na dare, Lahadi, 24 ga Satumba, 2023. .

“Yana cikin gidansa tare da iyalansa da ‘ya’yansa da mutanensa lokacin da ‘yan bindigar suka shigo, suka tilasta masa hawan babur.

“Mun samu wannan ci labarin mara dadi kuma mai girma Gwamna Hyacinth Alia ya riga ya ba da umarni tare da cikakken bayani ga jami’an tsaro don tabbatar da kwace sa daga wurin masu garkuwa da mutane.”

Firdausi Musa Dantsoho