Jakadan Italiya Mista Stefano Leo ya ziyarci Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike domin inganta harkokin kasuwanci.

0
28

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya sake jaddada kudirinsa na ganin birnin ya inganta a harkokin kasuwanci.

Nyesom Wike wanda ya ba da wannan tabbacin a lokacin da Jakadan Italiya a Najeriya, Mista Stefano Leo, ya ziyarce shi a Abuja, ya ce Hukumar za ta hada gwiwa da Italiya kan harkokin yawon bude ido da kuma bunkasa noma.

WIke ya ce da kansa zai ziyarci jakadan domin tattauna batutuwan da zasu amfana da Najeriya da Itali

Jakadan Italiya a Najeriya, Stefano Leo yayin da yake yiwa Wike fatan samun nasara a sabon aikinsa na ministan babban birnin tarayya Abuja, ya bayyana kwarin gwiwarsa na cewa zai yi aiki fiye da yadda ya yi a Rivers a matsayinsa na gwamna.

Ya ce Rome, babban birnin Italiya, ita ce kan gaba a fannin yawon bude ido, ya kara da cewa kasar na da manyan tsare-tsare na tallafawa ci gaban birni mai dorewa .

Jakadan ya ce wannan ziyarar na nufin za mu iya ci gaba da kyakkyawar haɗin kai. Ya kara da cewa zai yi farin cikin karbar bakuncin ministan a Ofishin Jakadancin na Italiya.

 

Daga Fatima Abubakar.