YANZU-YANZU EFCC ta cafke Tsohon Ministan Sufurin Jirage, Hadi Sirika kan zargin Badakalar Naira Bilyan 8 na sayen Jirgin Najeriya

0
20

Hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama Hadi Sirika, bisa zargin almubazzaranci da sama da Naira Biliyan 8 da ake alakantawa da badakalar Jirgin Najeriya.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, kan wani bincike da ake yi kan badakalar kudaden da suka kai N8,069,176,864.00.

 

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama wanda ake zargi ya bayyana a ofishin Hukumar EFCC na Babban Birnin Tarayya da misalin karfe 1:00 na ranar Talata.

Hukumar dai ta dadai tana bibiyar badakalar da ake zargin tsohon ministan.

Hadi sirika dai tsohon ministan jiragen sama ne a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Nigeria Muhammad Buhari tun daga 2015 zuwa 2023.

 

 

 

 

Hafsat Ibrahim