Kannywood: Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin rufe shagon sayar da maganin gargajiya

0
15

Kano/Press Release/Adamu

 

Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin rufe shagon sayar da maganin gargajiya

Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta ɗauki matakin gaggawa kan wani mai sayar da maganin gargajiya da ake zargi da amfani da wasu kananan yara a cikin wani talla mai ɗauke da kallaman da ba su dace ba.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Abdullahi Sani Suleman ya sanyawa hannu.

Hukumar ta bayar da umarnin rufe shagon mai sayar da maganin gargajiya biyo bayan Korafe-korafen da ta samu.

Haka kuma, Shugaban Hukumar Hukumar, Abba El-Mustapha, ya gayyaci mai saida Maganin wanda ake kira da Nagwale domin ya bayyana a gaban Hukumar domin amsa zarge-zargen da ake yi masa.

 

Da yake jawabi kan lamarin, Daraktan dake lura da sashin Dab’i na Hukumar Zakari garun Babba ya bayyana cewa sayarwa da kuma tallata irin waɗannan magunguna a bainar jama’a, musamman idan sun haɗa da yara ko abubuwan rashin kunya, laifi ne kuma yin hakan ka iya jawo tsauraran hukunci a ƙarƙashin doka.

Ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa tare da neman afuwa ga al’ummar Jihar Kano.

 

Adam Muhammad