An Sake Samun Ɓullar Cutar Korona (COVID-19) a Najeriya

0
13

An Sake Samun Ɓullar Cutar Korona (COVID-19) a Najeriya

 

Daga wakilin mu Gaddafi Isyaku Muhammad

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da samun sabon mai cutar korpna (COVID-19) bayan kusan shekaru uku babu rahoto.

Kwamishinan Lafiya na Calabar, Dakta Henry Ayuk, ya ce wanda ya kamu ɗin ɗan ƙasar China ne da ke aiki da kamfanin Lafarge, wanda ya shigo Najeriya a watan Maris amma ya fara nuna alamun cutar a watan Afrilu.

Bayanai sun ce an kai shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Calabar (UCTH), inda aka tabbatar da cutar, kuma yanzu yana samun sauƙi.

Hukumomi sun fara bin diddigin waɗanda suka yi hulɗa da shi domin killace su, tare da ƙarfafa matakan kariya domin hana yaduwar cutar.

 

Wallafawa Hafsat Ibrahim