*Gwamnan Kano ya yi Allah-wadai da daga dan kamfai da mata suka yi yayin Ziyarar Uwargidan Shugaban Ƙasa*

0
8

*Gwamnan Kano ya yi Allah-wadai da daga dan kamfai da mata suka yi yayin Ziyarar Uwargidan Shugaban Ƙasa*

 

Daga Adamu Muhammad Bichi

 

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nesanta kansa da gwamnatinsa tare da al’ummar jihar daga abin da ya bayyana a matsayin rashin da’a da wasu mata suka yi yayin ziyarar aikin da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta kawo jihar.Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Mustapha Muhammad, ya sanyawa hannu.

Sanarwar ta ce Gwamnan ya nuna takaicinsa ne yayin taron addu’a ta musamman karo na uku domin neman zaman lafiya mai ɗorewa, wanda aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Kano.

A cewar sanarwar, mahaddata Alƙur’ani 4,444 ne suka hallara domin neman taimakon Ubangiji kan zaman lafiya da ci gaban jihar da ƙasa baki ɗaya.

Gwamna Yusuf ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa da kuma kaucewa kyawawan dabi’u da manufofin *Kano First* *Agenda* ke koyarwa.

Ya ce irin wannan aiki ya saɓa da koyarwar addinin Musulunci, wanda ke umarni da kamun kai da girmama shugabanni.

Gwamnan yasa an kawo masa matasan da suka aikata hakan tare da yi musu gargaɗi kan duk wani abu makamancin haka a nan gaba da zai iya bata sunan jihar.

Haka kuma, ya gargadi ‘yan siyasa da su daina amfani da matasa wajen cimma muradansu siyasa marasa kyau .

“Ina kira ga abokan harkata na siyasa da su jagoranci al’umma da kyawawan misalai, su daina siyasar zagi, su maida hankali kan ci gaban Kano maimakon tunzura yara zuwa rashin tarbiyya,” in ji Gwamnan.

 

Ya kuma bukaci wadanda suka aikata lamarin da su nemi gafarar Allah tare da ba al’ummar Kano hakuri kan kunyar da suka jawo wa jihar.

 

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da Kano ta kasance cibiyar tarbiyya, karamci da riko da addini.

 

Ya kuma sake jaddada kudirin gwamnati na bai wa matasa kulawa da tarbiyya tare da kare kyawawan al’adun jihar Kano.

Idan za a iya tunawa a Ranar Alhamis din data gabata ne, yayin ziyarar da matar shugaban Kasa ta kawo jihar Kano, aka hangi wasu mata suna daga Dan kamfai, Wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin al’umma.

 

Wallafawa Hafsat Ibrahim kawo