A cikin wata takarda mai dauke da hotunan bayanai da aka rabawa jama’a, jami’an lafiya sun bayyana cewa cutar Hantavirus na yaduwa ne musamman ta hanyar hulda da fitsari, da kashin bera ko yawunsa.
Sun ce idan ba a gano cutar da wuri ba tare da fara magani ba, tana iya haifar da matsananciyar matsalar numfashi.
Jami’an sun bayyana wasu manyan alamomin cutar da ya kamata jama’a su lura da su, ciki har da zazzabi mai tsanani tare da sanyi, da gajiya mai yawa da ciwon tsoka, da jiri, da ciwon kai, da wahalar numfashi, da kuma tashin zuciya ko ciwon ciki.
An shawarci jama’a da su garzaya asibiti cikin gaggawa idan suka fara ganin irin wadannan alamomi bayan sun yi hulda da beraye ko wuraren da suke.
Domin dakile yaduwar cutar, NCDC ta bayyana matakan kariya guda shida da suka hada da tsaftace gida tare da hana beraye shiga, adana abinci a cikin mazubi masu murfi, fesa maganin kashe kwayoyin cuta a wuraren da beraye suka yin kashi kafin tsaftacewa, amfani da safar hannu da takunkumin fuska yayin tsaftacewa, kai rahoton yawaitar beraye ga jami’an lafiya, da kuma neman kulawar likita cikin gaggawa idan an yi hulda da beraye.
Sanarwar ta kuma jaddada muhimmancin bin ka’idojin tsafta kamar wanke hannu, sanya takunkumin fuska da kiyaye tazara a matsayin wani bangare na kokarin kare al’umma.
Adamu Muhammad

Hukumar Yaki da Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC), tare da hadin gwiwar Hukumar Yaki da Yaduwar Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC), sun fitar da sanarwar wayar da kan jama’a inda suka bukaci mazauna jihar su dauki matakan kariya daga cutar Hantavirus, wata mummunar cuta da ake yadawa ta hanyar hulda da beraye.

