HACKERS SUN SHIGA DATABASE NA ZENITH BANK, SUN SACE BAYANAN WASU KWASTOMOMI

0
3

’Yan dandatsa na intanet (hackers) sun kai hari kan bayanan Zenith Bank, daya daga cikin manyan bankunan kasuwanci a Najeriya, inda suka samu damar shiga wasu bayanan kwastomomin bankin.

Zenith Bank ya tabbatar da faruwar harin ne a cikin wani sakon imel da ya aikewa kwastomominsa ranar Talata, inda ya bayyana cewa an samu kutse cikin tsarin bayanan bankin.

A cewar bankin, ’yan dandatsan sun samu damar samun wasu bayanan kwastomomi da suka hada da adiresoshin imel da lambobin wayoyi yayin wani harin yanar gizo da ya kasance wani bangare na gagarumin harin da ake kai wa kungiyoyi da hukumomi a sassa daban-daban na duniya.

Bankin ya jaddada cewa bayanan da aka samu ba su da yawa, yana mai cewa harin bai shafi muhimman ayyukan bankin ko hanyoyin gudanar da harkokin banki na zamani ba.

Zenith Bank ya ce ayyukan banki da hanyoyin sadarwar sa na zamani suna nan cikin tsaro kuma suna aiki yadda ya kamata, duk da harin da aka kai kan wasu bayanan kwastomomi.

Bankin ya kuma bayyana cewa ya fara gudanar da bincike domin gano cikakken yanayin harin, inda ya ce an kunna dukkan matakan da aka tanada domin tunkarar irin wannan matsala da sauran matakan kariya daga hare-haren yanar gizo nan take bayan gano kutse cikin tsarin.

A cikin sakon da ya aikewa kwastomominsa, bankin ya bukaci jama’a da su kara taka-tsantsan domin kauce wa fadawa hannun masu damfara da za su iya amfani da bayanan da aka samu wajen aikata laifukan yanar gizo.

Bankin ya shawarci kwastomominsa da su yi hattara da sakonnin imel, sakonnin waya (SMS) ko kiran waya da ba su sani ba, musamman wadanda za su nemi bayanan sirri na asusun banki.

Zenith Bank ya kuma gargadi kwastomomi da kada su taba bai wa wani kalmar sirri (Password), lambar sirri ta ATM (PIN), One-Time Password (OTP), ko wasu bayanan tsaro na asusunsu.

Bankin ya ce bai kamata kwastomomi su bayyana irin wadannan bayanai ga kowa ba, ko da kuwa wanda ya kira su ya bayyana kansa a matsayin ma’aikacin banki.

Harin ya sake jawo hankali kan bukatar karfafa tsaron bayanan kwastomomi da tsarin bankuna a Najeriya, musamman a wannan lokaci da harkokin banki ke kara dogaro da fasahar zamani.