Abubuwan da aka tattaunawa a taron Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas (NEGF) 

0
22

Sanarwar Bayan Taron Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Maso Gabas (NEGF) Karo Na 10 Da Aka Yi A Bauchi Jiya Juma’a .

 

Daga Yunusa Isah kumo

Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa Maso Gabas (NEGF), data ƙunshi Gwamnonin Jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe ta kammala taronta karo na 10 jiya Juma’a 17 ga watan Mayun 2024 a Bauchi babban birnin Jihar Bauchi.

Ƙungiyar ta bayyana farin cikinta kan yadda haɗin gwiwa tsakanin jihohin yankin ke bunƙasa tare da yabawa da irin nasarorin da take samu bisa salon jagorancin gwamnonin jihohin.

Kungiyar ta jaddada ƙudurinta na samar da manufa guda tare da bin tafarki bai ɗaya don amfanin al’ummarsu.

Bayan kammala tattaunawa, ƙungiyar ta gabatar da sanarwa kamar haka:

1. Gwamnonin sun amince cewa karan ƙungiyar ya kai tsaiko; ganin yadda har ta gudanar da taronta karo na 10, lamarin dake nuni da cewa jihohi da gwamnonin suna kan turba mai kyau, don haka ya kamata su tabbatar da ɗorewar hakan.

2. Ƙungiyar ta yabawa Gwamnatin Jihar Bauchi bisa gudanar da bikin baje kolin kasuwanci na yankin Arewa Maso Gabas, biyo bayan shawarar da ƙungiyar ta yanke a taronta karo na 8 a Maiduguri.

Baje kolin kasuwanci wani muhimmin abu ne da zai inganta kasuwanci a yankin, da buɗe ƙofofin yankin ga masu zuba jari, uwa uba kuma wani tabbaci ne cewa ƙungiyar tana iya aiwatar da shawarwarin data yanke.

3. Ƙungiyar ta sake jaddada damuwarta kan yadda gwamnatin tarayya ke nuna halin ko in kula ga yankin na Arewa Maso Gabas wajen samar da manyan ayyukan raya ƙasa. Tace duk da kukan da take yi na ganin an mai da hankali kan yanayin samar da ababen more rayuwa a yankin dake ci gaba da bayyana ra’ayoyinsa a cikin dukkanin sanarwar da yake fitarwa tsawon shekaru, musamman rashin kyawun hanyoyin mota dana jiragen ƙasa dake haɗe yankin Arewa Maso Gabas da sauran yankunan kasar, babu wani abun kirkin da ake yiwa yankin.

Hanyoyi da titin jirgin ƙasa na Enugu zuwa Maiduguri suna cikin mawuyacin hali duba da yadda suka lalace. Wannar wata babbar hanya ce ta kasuwanci a yankin kuma tana da matuƙar muhimmanci ga haɗin kai, da samar da zaman lafiya da inganta haɗin kan ƙasa.

Haka kuma ba a sanya yankin ba cikin shirin samar da ababen more rayuwa na ƙasa don sauya amfani da man fetur zuwa iskar gas.

Kungiyar tana ƙira ga Gwamnatin Tarayya ta duba halin da yankin ke ciki, tare da sake gina waɗannan muhimman ababen more rayuwa musamman hanyar jirgin ƙasan ta Enugu zuwa Maiduguri dake da muhimmanci wajen haɓakar tattalin arziƙi, ta kuma shigar da yankin na Arewa Maso Gabas cikin dukkanin tsare-tsarenta na ƙasa.

4. Ƙungiyar ta kuma bayyana takaici da ɓacin rai kan halin da yankin ya samu kansa cikin wata guda da ya gabata na rashin wutar lantarki da kuma halin ko oho da kamfanin tura wuta na TCN ke nunawa wajen magance wannan lamari mai matuƙar muhimmanci ga tsaro da ci gaban ƙasa.

Ƙungiyar tana sanya ido sosai kan alƙawarin da kamfanin ya yi na maido da wutar lantarki a dukkan jihohin yankin nan da ranar 27 ga wannan wata na Mayun 2024; don haka ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta umarci kamfanin na TCN ya ɗauki matakin gaggawa kan lamarin.

Kungiyar ta kuma cimma matsaya cewa cikin ƙanƙanin lokaci zata kafa wata tashar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana wacce za ta iya samar da aƙalla Megawatts 10 a kowace Jiha.

 

5. Ƙungiyar ta nuna matuƙar damuwa cewa Arewa Maso Gabas, shine yanki ɗaya tilo a Najeriya dake da layin tura wuta ɗaya kacal dake sada jihohi shida na yankin da wutar lantarki a yankin mai faɗin kusan kilomita murabba’i 300,000 da al’umma fiye da miliyan 35.

Wannan ya sanya yankin ya zama mafi rauni kuma mafi ƙarancin ci gaban masana’antu da haɓakar tattalin arziƙi duk da cewa fiye da kaso 70 cikin ɗari na al’ummarsa ƴan ƙasa da shekaru 35 ne.

Don haka ƙungiyar ta yi ƙira ga Ministan Wutar Lantarki da kuma Gwamnatin Tarayya su gaggauta gyara layin wutar lantarki mai karfin KV 330 daga Makurdi –zuwa Gassol zuwa Jalingo dake haɗewa har jihohin Adamawa zuwa Gombe zuwa Bauchi da kuma tsawaita layin wutar mai ƙarfin KV 330 daga Kano zuwa Bauchi zuwa Yobe, mai haɗewa da Jihar Borno.

6. Ƙungiyar ta ƙuduri aniyar ƙara yawan makamashin da ake samu a madatsar ruwa ta Kashimbilla da Daɗinkowa waɗanda yankin baya amfana da su saboda ma’aikatar wutar lantarki ta gaza haɗe su da layin wutan Makurdi zuwa Gassol zuwa Jalingo mai karfin KV 330.

7. Ƙungiyar tace ana ganin tasiri da illar sauyin yanayi da taɓarɓarewar muhalli ƙarara a yankin, tana mai yabawa jihohin yankin saboda matakan da suke ɗauka don farfaɗo da muhallin. Ta kuma yi ƙira da a ƙara ƙaimi da haɗin kai a yankin don daƙile ƙaruwar kwararowar hamada a yankin.

 

8. Ƙungiyar ta buƙaci Hukumar Bunƙasa Arewa Maso Gabas (NEDC) ta riƙa tuntuɓan masu ruwa da tsaki a cikin harkokinta. Ta yi ƙira ga hukumar ta riƙa aiki tare da jihohin yankin don bunƙasa makamashi tare da buɗe hanyoyin samar da makamashi a yankin da kuma rage ƙarancin makamashin dake damun jama’a.

 

9. Ƙungiyar ta lura cewa duniya tana fama mummunar matsalar rashin abinci, musamman duba da yaƙin Ukraine, da sauyin yanayi da rashin samun damar yin noma a Arewa Maso Gabas, hakan yasa jihohin yankin suka ƙuduri aniyar ci gaba da zuba jari a harkokin noma da karfafa ƙananan masana’antun noma zuwa matsakaitan masana’antu.

Jihohi mambobin ƙungiyar za su tallafa wajen sayo ingantattun iri masu jure fari da saurin nuna, da bada tallafin takin zamani da tabbatar da cewa yankin ya yi fice wajen samar da irin wadannan iri.

 

10. Ƙungiyar ta kuma yanke shawarar yin haɗin gwiwa da kamfanin OCP Africa don tallafawa harkokin noma a yankin na arewa maso gabas.

 

11. Ƙungiyar ta jaddada ƙudurinta na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jihohi mambobin ƙungiyar da asusun tallafawa yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF kan zuba jari don dorewar shirin samar da ingantaccen ruwa da tsaftar muhalli na (WASH) a yankin.

12. Ƙungiyar ta yabawa gwamnati da al’ummar Jihar Bauchi bisa ɗaukar nauyi da gudanar da taron cikin nasara. Ta kuma ƙuduri aniyar gudanar da taronta na gaba karo na 11 a Damaturu, Babban Birnin Jihar Yobe tsakanin 30 zuwa 31 ga watan Augustan 2024.

 

SANARWA:

Farfesa Babagana Umara Zulum, CON, mni, FNSE

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Maso Gabas kuma Gwamnan Jihar Borno.

 

 

Hafsat Ibrahim