AFCON 2021: Ahmed Musa ya bar sansanin Super Eagles

0
103

Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, ya fice daga sansanin atisayen tunkarar gasar cin kofin Afrika ta 2021.

Musa bai buga atisayen karshe na kungiyar ba a ranar Laraba, bayan da ya rasa dan uwa.

 An baiwa dan wasan izinin barin stadium in Fatih Karagumruk na kasar Turkiyya domin kasancewa tare da danginsa sakamakon rashin da sukayi

 Dan wasan mai shekaru 28, zai bi sahun sauran ‘yan wasan da ke Kamaru gabanin wasan farko da Najeriya za ta yi da Masar ranar 11 ga watan Janairu.

Dan wasan mai shekaru 28, zai bi sahun sauran ‘yan wasan da ke Kamaru gabanin wasan farko da Najeriya za ta yi da Masar ranar 11 ga watan Janairu.

  A halin da ake ciki kuma, wani dan wasan gaba, Odion Ighalo, ba zai halarci gasar ba, sakamakon kin amincewar da kungiyar Al-Shabab ta yi na sakin shi.

 Wata magana da yayyi a cikin kwantiragin da ya kulla da kulob din na Saudiyya, yayi nuni da cewa ba ya taka leda a Najeriya, a yanzu, hakan ya hana shi shiga gasar.

 

 An sake kiran Ighalo zuwa Super Eagles a watan Nuwamba bayan da ya sanar da yin murabus tun da farko kuma ya shafe sama da shekaru biyu baya kungiyar.

  By: Firdausi Musa Dantsoho