AMFANIN MADARAN WAKEN SUYA GA LAFIYAR DAN ADAM

0
1566

Madaran waken suya na daya daga cikin hanyoyin da akafi sani na kiwon lafiya masu gina jiki,waken suya na dauke da wasu sinadarai wanda keda matukar muhimmanci ga lafiyar dan Adam.babban abun ciki shine protein da kuma vitamin.

Waken suya na daya daga cikin abinci marasa illa,muddin bakada lahani ga waken suya zaka iya shan madararsa, shan karamar kofi 1 na madaran waken suya a kowace rana babban hanya ne na samun wasu fa’idodin lafiyarka. 

Maganin da madaran waken suya keyi sun hada da: 

Maganin ciwon kwakwalwa:

Madaran waken suya na iya taimakawa wajen rage hadarin dake kai domin yana kunshe da maganin kananan kwayoyin cuta tare da fa’idodin lafiyar kwakwalwa. Madarar waken suya na iya taimakawa wajen hanawa da magance rikicewar yanayin damuwa.

Rigakafin ciwon kansa:

Kamar yadda calcium ke taimakawa wajen rage hana cututtukan kansan hanji haka zalika madaran waken suya na taimakawa wajen rigakafin cutar kansa , yana taimakawa wajen kawarda cututtukan da ke haifar da cutar kansa daga jikin dan Adam.

Ciwon zuciya:

Cutar zuciya itace babbar matsalar lafiyar maza, ana shawartan maza da su ci abinci mara nauyi mai kyau da protein don hana matsalolin zuciya da jijiyoyin jini, kofi daya na madaran waken suya ya kunshi protein, kuzari da kuma wadataccen mai. Haka zalika madaran waken suya na inganta lafiyar jini da matakan cholesterol. 

DAGA:UMMU-KHULTHUM ABDULKADIR