An kai hari kan ayarin dan takarar kujerar Gwamna a karkashin jam’iyyar PDP na jahar Zamfara, Dr Dauda Lawal Dare.

0
136

Dan takarar gwamnan jihar Zamfara a karkashin jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa na 2023, Dakta Dauda Lawal, ya yi Allah-wadai da harin da wasu ‘yan daba da gwamnatin jihar suka dauka a kan ‘ya’yan jam’iyyar.

Ya bayyana harin a matsayin kololuwar rashin bin doka da oda, da kuma tada zaune tsaye da ka iya kawo rashin jituwa a jihar.

Lawal a wata sanarwa da cibiyar watsa labarai ta Dauda Lawal da ke Gusau ta fitar a ranar Asabar din da ta gabata, ya jaddada cewa wasu ‘yan baranda dauke da makamai sun kai masa hari a daren Juma’a yayin da suke shiga babban birnin jihar Zamfara – Gusau.

Sanarwar ta kara da cewa: “Muna cikin mawuyacin hali. Abin takaici, mun sami kanmu a cikin wannan rikici. Mun yi tunanin ‘yan daba ’yan sun zama tarihi a jihar, amma APC da gwamnatin jihar sun tayar da shi.

“Ya ce an san jam’iyyar PDP da  bin doka da oda, mu jam’iyya ce mai matukar aiki da bin dokar jihar. Wannan dalilin ne ya sa muka jira hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta dage haramcin yakin neman zaben gwamna kafin shirya duk wani abu da ya shafi siyasa a jihar Zamfara.

“PDP ta ware 15 ga Oktoba a matsayin ranar da za ta karbi dubban ‘yan APC da suka sauya sheka zuwa PDP tare da kaddamar da majalisar yakin neman zaben gwamna a 2023.

“Yan baranda da jam’iyyar APC da gwamnan jihar suka dauki nauyin kai wa tawagarmu hari ne a hanyarmu ta zuwa Gusau. An farfasa motoci da yawa tare da kone su a yayin harin.

“yan barandan karkashin jagorancin wani Aliyu Alhazai Shinkafi, tsohon shugaban kwamitin yaki da ‘yan daba na Zamfara kuma kwamandan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Zamfara (ZAROTA) suka kai hari gidan dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP. Alhazai ya jagoranci ‘yan daba sun tare hanyar zuwa gidan Lawal da wurin da yake zaune, inda suka kafa ma’auni na kai harin. A sabon harin da aka kai na ba gaira ba dalili, an lalata motocin yakinmu na yakin neman zabe tare da kwasar ganima.

Mutanen jahar Zamfara sun gaji mulkin kama karya da jam’iyyar APC ta jahar Zamfara karkashin jagorancin gwamna Mohammed Bello Matawalle.

“Dr Dauda Lawal Dare,yayi kira ga Sufeto Janar na ‘yan sanda ,da darakta General na DSS da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki da su kawo dauki tare da dakatar da Gwamnan jahar da mukarraban sa wurin kawo karshen wannan tashin hankula kafin a fara kamfen.

 

  1. Daga Fatima Abubakar.