An rushe sarakunan jihar Kano

0
27

Majalisar dokokin jihar Kano Amince inda ta rushe sarakuna biyar baki daya a jihar.

Hakan na nuni da cewar yanzu haka babu sarki a jihar Kano, wanda za’a kira masu naɗa Sarki.

Muna tafe da karin bayani a labaran mu na gaba.

 

Idan zaku tuna dai Mujallar Tozali ta rawaito muku céwa majalisar ta Amince da farko an  yi shirin sauke wadannan sarakunan cikin kwanaki 20 da rantsar da wannan gwamnatin. Amma a yau  Alhamis, akwai wani zama na musamman da majalisar za ta yi domin amincewa da sauyin.

Yanzu haka ana fargabar barkewar bore ko kuma zanga-zanga musamman daga ɓangaren jama’ar da wannan tsarin bai yi musu daɗi ba a jihar ta Kano.

kuma ta Amince da sauke sarakunan.

‘Yan majalisar Dokokin Kano na APC sun yi watsi da rushe masarautun Kano da majalisar dokokin tayi

Sunyi watsi da hakan ne jim kadan bayan da majalisar ta amince gyaran dokar rushe masarautun.

 

 

 

Hafsat Ibrahim