babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin daurin rai da rai kan Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) da ake zargi da aikata laifuka da dama da suka shafi ta’addanci.
Mai shari’a James Omotosho, wanda ke jagorantar shari’ar, ya fara samun Kanu da laifuka biyu da ke da alaka da aikata ta’addanci. Kotun ta ce ya sha bayyana umarnin zama a gida da ya yi, tare da barazanar tashin hankali da kashe-kashe da ake yi ta kafafen yada labarai daban-daban, ya Jagorancin ta’addanci a karkashin dokokin da suka saba.
Yayin da ake ci gaba da shari’ar, Mai Shari a ya kuma yanke hukunci kan wasu tuhume-tuhume guda uku, inda ya samu Kanu da laifin zama jagoran haramtacciyar kungiyar da kuma tunzura mabiyansa su tayar da hankali. Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun gabatar da shaidun da ke nuna cewa Kanu ya ci gaba da zama mamba a kungiyar IPOB da kuma reshenta, Eastern Security Network (ESN), duk da haramcin da aka yi musu.
Kotun ta ci gaba da cewa watsa shirye-shiryen da ake dangantawa da Kanu Wanda yanuna suna karfafa hare-haren da suka kai ga mutuwar jami’an tsaro da lalata wuraren jama’a ciki har da ofisoshin ‘yan sanda.
Jaridar Guardian ta ruwaito cewa tun farko mai shari’a Omotosho ya bada umarnin a fitar da Kanu daga kotun bayan ya nuna rashin da’a a lokacin da ake shari’a.
A baya dai alkalin kotun ya yi watsi da wasu sabbin kararraki guda uku da Kanu ya shigar, inda ya bayyana cewa ba su da cancanta. An gabatar da korafe korafen ne bayan an riga an dage shari’ar don yanke hukunci.
Yayin da mai shari’a Omotosho ya kai ga yanke hukuncin, Kanu ya nuna rashin amincewarsa, inda ya jaddada cewa kotun ba za ta iya ci gaba ba , saboda bai gabatar da jawabinsa na karshe a rubuce ba. Daga baya Kuma ya daga muryarsa, yana zargi alkalin da nuna son kai kuma ya ce kotun “ba ta san doka ba”.
Biyo bayan ficewar. Sai mai shari’a Omotosho ya umarci jami’an tsaro da su cire Kanu daga harabar kotun. Alkali ya ci gaba da karanta hukuncin karshe a bayansa.
Hafsat Ibrahim


