Ministan ya bayyana hakan a yayin kaddamar da aikin gina titin Abuja, ya ce tafiyar tasa ta baya domin hutu, ba don neman magani ba. Ya kuma zargi masu yada wannan jita-jita da siyasa mara amfani, inda ya yi musu addu’ar rashin lafiya tare da tabbatar zai ci gaba da aiki. “Kun ga yadda kasar nan take, siyasa muke yi da komai, ta yaya wani zai zauna kawai ya rika fadin abubuwa iri-iri?
A makon da ya gabata ne ake ta yada rahoton cewa daya daga ministoci a gwamnatin Bola Tinubu ya tafi jinya London. Wasu majiyoyi sun ce Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ba shi da lafiya sosai wanda ta kai ya bar kasar neman lafiya.
Sai dai minista Wike ya yi magana kan jita-jitar da ake yadawa a wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zuminta
Majiyoyi sun ruwaito cewa Wike ya yi tafiya zuwa Birtaniya a baya-bayan nan, amma aka yada jita-jitar cewa ya yi tafiyar ce domin neman magani. Jita-jitar ta ce Wike na fama da ciwon zuciya sai dai a wancan kwanaki ministan bai yi martani ko daga bakin hadiminsa ba kan haka.
Daga karshe Wike ya kuma caccaki masu yada jita-jitar, inda ya yi musu addu’ar samun rashin lafiya maimakon shi da ake yi wa fatan samun rashin lafiya. Ya kara da cewa: “Allah zai ci gaba da taimaka musu su samu bugun zuciya. Wannan shi ne addu’ata, zan sa hannu a gaisuwar mutuwa. Ba da jimawa ba zan gaya musu cewa muna ba su hakuri. Muna son su, amma su yi hakuri.”..
Hafsat Ibrahim


