An Saki Tsohon Minista Ikira Aliyu Bilbis Daga Gidan Yari

0
18

An saki tsohon ministan yada labarai, Alhaji Ikra Aliyu Bilbis daga gidan yari. Naija News ta ruwaito cewa an damke jigo na jam’iyyar PDP da ke neman kujerar Sanata a Zamfara ta tsakiya a zaben 2023 makonnin da suka gabata.

Nan take aka gurfanar da shi a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta 11 ta Jihar Zamfara, bisa zarginsa da laifin hada baki da hargitsa jama’a. Ana zargin dan siyasar da yin tasiri wajen lalata allunan tallace-tallacen jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da wasu kadarori a jihar. Sai dai an sake Bilbis ne kwanaki da suka gabata a karkashin kalubalan samar da sakatariyar dindindin a ma’aikatan gwamnati da kuma wanda ke da gida a garin Gusau wanda ya kai N20m a matsayin wanda zai tsaya masa.

Tsohon ministar ya ci gaba da kasancewa a tsare  bayan bai cika sharuddan da aka gindaya masa ba. Ko da yake, a ranar Laraba, 14 ga Disamba, 2022, Bilbis ya sake samun ‘yanci yayin da kotu ta ba da damar a sake shi ba tare da wani sharadi ba.

Mai baiwa jam’iyyar PDP shawara kan harkokin shari’a, Barista Shehu Ajiya, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai. “An bayar da belin tsohon  ministan ba tare da wani sharadi ba. “A ci gaba da sauraron karar a ranar 13 ga watan Disamba, alkalin kotun bai zo kotun ba amma daga baya ya aika da sanarwar sakinsa ba tare da wani sharadi ba,” in ji Ajiya. A cewar mai baiwa PDP shawara kan harkokin shari’a, an dage shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Disamba, 2022, domin sauraren wata kwakkwarar karar.

Daga:Firdausi Musa Dantsoho