An samu barkewar tashin hankali a dei-dei tsakanin ‘yan babura,da yayi sanadiyar mutuwar wasu mutane

0
118

Wani hadarin babur da ya afku a garin Dei-Dei da ke unguwar da ke kusa da babbar hanyar Kubwa a Abuja , ya haifar da kazamin tarzoma, wanda ya yi sanadin kashe akalla mutane biyu,tare da kona babura da kuma  motoci da dama a yankin.

An tattaro cewa rikicin ya barke ne bayan da wani direban babur (Okada) ya yar  da wata mata a bakin hanya kusa da rumbun katako a yankin wacce trailer ya taka ta inda yayi sanadiyar mutuwar ta.

A cewar wani ganau, lamarin ya janyo cece-kuce a tsakanin direban babur din da kuma ‘yan kallo, inda suka yi ta yawo a wurin da hadarin ya faru, kwatsam direban babur din ya fito da wuka ya daba wa mutane biyar.

Da yake ba da labarin faruwar lamarin, wani ganau ya ce, “A lokacin da na isa wurin domin shiga motar bas zuwa gari, sai na gamu da mutane suna ta cece-kuce suna yi wa kansu ihu, a gaban shagunan kwanar da ke kusa da mahadar Tumatir, daura da Timber Shed, kuma kafin in fahimci me ke faruwa kawai sai suka fara fada.

“Daga baya na gano cewa daya daga cikin mutanen da ke jayayya an daba masa wuka a kai kuma ya mutu nan take, wanda hakan ya kara haifar da martani, wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu.”

Hakazalika, wani ganau wanda ya bayyana sunansa Obinna, ya ce a lokacin da ya isa wurin, ya ga gawarwaki biyu da babura biyar, ciki har da wasu motoci da aka farfasa.

An kuma tattaro cewa yayin da rikicin ke gudana kan babban titin da ke kan hanyar zuwa wasu yankuna ya cika da cunkoson ababen hawa, inda mutane suka makale yayin da wasu ke barin ababen hawan su suna gudu.

Sai dai an shawo kan lamarin, bayan da tawagar hadin gwiwa ta ‘yan sandan Mobile da sauran jami’an tsaro da aka tura yankin suka shiga tsakani a kan lokaci, inda wasu daga cikin jami’an tsaro kuma suka samu raunuka.

Fatima Abubakar