Gobe Lahadi karfe 7 na safe Shugaban kasa Bola Tinubu zai yi wa Yan Najeriya jawabi

0
5

*Breaking*…..

Shugaban kasa Bola Ahmed zai gabatar da jawabi ga yan kasar nan kai tsaye dangane da halin da ake ciki da kuma kiraye kirayen da yan kasa suka mika masa.

Mai magana da ywun shugaban kasa Ajuri Ngalele ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin sada zumunta, yana mai cewa jawabin shugaban kasar zai gudana ne da karfe 7 na safiyar Gobe Lahadi.

Za a haska jawaban kai tsaye a gidan talabijin na kasa NTA sai ku tara domin jin tarin albishir da zai yiwa yan kasa ko akasin haka.