An yi garkuwa da Uwargidan mataimakin kwamanda Janar na NSCDC reshen jahar Nasarawa.

0
14

Uwargidan Kwamandan Rundunar civil Defence na Kwamand da ke Nasarawa,Apolos Dandaura, an yi garkuwa da matar sa ne a ranar Larabar da ta gabata, sannan aka harbe kaninsa a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

An tattaro cewa,kanin mataimakin kwamanda, Apolos Dandaura, yanzu haka yana jinya a wani asibiti mai zaman kansa da ke Lafia, inda aka ce yana karbar magani.

An yi garkuwa da matar Kwamandan, a unguwar Shenge da ke Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar NSCDC reshen jihar Nasarawa, Jerry Victor, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho, ya ce har yanzu ba a san inda lamarin ya faru ba.Babu dai cikakkun bayanai yayin hada wannan rahoto.

Daga Fatima Abubakar.