Yadda Za Ku Lura Da Fatan Ku Gabanin Zuwan Hunturu

0
92
Lokacin huntru wanda ke faruwa tsakanin November zuwa February na zuwa da busasshen iska da kura, hakan na shafar fatar mu ta hanyoyi daban-daban kamar bushewar fata, fashewar labe har fashewar kafa da cututuka da dama.
Yana da mahimmanci ku kasance da kula da fatar ku wanan lokaci na hunturu.
Da farko dai a sha ruwa da yawa aklla lita daya da rabi a ko wane yini, yin hakan zai taimaka wajen fitar da kazanta da sa fatar jikinku ta yi laushi sanan a ci ya’yan itatuwa da kayan marmari masu yawa.
A sha zuma, lemun tsami, cita da ruwan zafi ko dumi don bushewar makogwaro da za’a iya fuskanta a lokacin huntru.
Ayi wanka da sabulu da zai sa fata danshi wato moisturizer sanan a shafa mayuka mai moisturizer da kuma mayukan mai wato essential oils da ya dace da fatar ku, kama irin su man kwakwa, man zaitun, man kadanya da man almond da kuma mayuka masu hadi da lactic acid, glycerin, mineral oil da petroleum; su ne za su hana fatar ku bushewa.
Kar ku bari fatar ku ya bushe kafin a shafa mai wato bayan an fito daga wanka. Jiki da danshi ko kuma da dan sauran ruwan wanka ya fi a shafa ma sa mai, hakan zai sa fatar ya sha mai yadda ya kamata kuma yayi laushi; Yin hakan jiki ba zai samu tamoji ba wato wrinkles.
Ku guji mayuka masu digon barasa a cikin su wato alcohol domin yana sa fata bushewa, ku kuma guji ruwan zafi sosai don zai tase man da ke fata ya kara bushewa.
Ku motsa jikin ku don zai taimaka wa lafiyan hankali da jiki, don lafiyan jiki da hankali na shafar fata. Yin amfani da mayuka kama dilka wato exfoliating scrubs wajen goge jiki yayi laushi da cire bushenshen fatar da ya mutu wato dead skin cells jifa jifa, domin yawan hakan zai cire man da ke cikin fata wanda hakan zai haifar da bushewar fata.
Ku yi amfani da mayuka masu sa jiki danshi sosai wato moisturizing creams, lotion ko mayukan mai essential oils.
Safrat Gani