Babu adadin tsoratarwa da zai hana mu aiki .In ji Wike

0
6

••• Ya kafa kwamitin mutum bakwai  don tattaunawa da shugabannin Ruga

Da yammacin ranar Lahadi ne ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya shiga cikin al’ummar Ruga da ke gundumar Wuye.

Wike wanda ya Isa rugan da misalin karfe shida da minti 17 na  yammacin lahadi 10 ga watan Nuwamba, yayi jawabi ga mutanen da aka rushe matsugunin su tun ranar Juma’an da ta wuce.

Bayan ya yi wa jama’a jawabi, ya kafa kwamitin mutum bakwai na hukumomin tsaro, Daraktan filaye da daraktan kula da raya kasa don tattaunawa da tawagar mutane biyar na shugabannin Ruga don ba da shawarwari da kulawar  gwamnati.

A halin yanzu, Wike ya ba da umarnin cewa har izuwa lokacin da kwamitin zai Ida Zama ba za a sake wani  gini na dindindin ko na wucin gadi a wurin da aka rushen ba

Bayan ya yi magana da mazauna Ruga cikin harshen turanci pidgen, Wike ya yi jawabi ga ‘yan jaridun da suka tafi tare da shi:

Ya ce,“Wannan fili  na gwamnati ne ,kuma batun kwace fili kamar yadda ake zargi bai taso ba.

A kalaman sa, ya ce “Gwamnati ta yanke shawarar cewa za mu binciki lamarin kuma mu fito da matsaya ta karshe. Babu wani nau’i na  tsoratarwa da cin zarafi da zai hana mu aiki, dole ne mu yi aikinmu, ba ruwanmu da wanda kuke ɗauka, kuna kiran su ƙungiyoyin jama’a domin su ba ta mana suna.Manufarmu ita ce mu kare rayuka da dukiyoyi da kuma ceto Abuja don zama daya daga cikin birane mafi kyau a duniya.”

Idan dai za a iya tunawa a ranar Asabar ne wata kungiyar farar hula ta hada al’umman ruga da ke Wuye ,domin gudanar da zanga-zangar adawa da ruguza matsugunin su da aka gina ba bisa ka’ida ba.

Wike ya kuma ba da tabbacin cewa za a ruguza duk sauran gidajen da ke zama barazana ga tsaro a babban birnin tarayya Abuja.

Tun da farko shugaban mazauna garin Abba Garo ya roki ministan da ya duba halin da suke ciki ya yi musu wani abu.

Garo ya shaida wa ministan cewa rusau na karshe a ranar Juma’a shi ne karo na 22 da ake ruguza al’ummar.

Ya ce su kusan mutane 10,000 ne a cikin al’umman da suke zaune. Ya ce ya shafe shekaru 37 a nan kuma ba wai suna neman su mallaki filin ba ne ko Kuma su fi karfin Gwamnati.

Ya ce suna ba da dama a duk lokacin da ci gaba kamar yadda filin Jirgin na kasa ya riske su,

Ya roki ministan “Don Allah da ya taimaka a ba mu matsuguni inda za su zauna.

 

Daga Abuja.

Fatima Abubakar.