Ministan babban birnin tarayya Abuja ya shaida wa Gwamnonin jam’iyyar PDP a ranar Laraba cewa, ba wanda zai iya tsoratar da shi ,yayin da ya yi gargadin a kan duk wani magudin zabe a jihar Ribas.
Ministan ya bayyana hakan ne bayan wata ganawar sirri da ya yi da mambobin kungiyar gwamnonin PDP karkashin jagorancin shugaban kuma gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed a ziyarar ban girma da suka kai ofishin ministan, tare da rakiyar gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri. Gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang, da gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas.
Idan dai za a tuna a ranar Litinin ne rikici ya barke a jihar Ribas, bayan yunkurin da majalisar dokokin jihar ta yi na tsige gwamna mai ci, Siminalayi Fubara.
Sai dai Wike a lokacin da yake jawabi ga Gwamnonin PDP, ya ce ba zai ji tsoro ba, yana mai cewa yunkurin tsige shi bai yi daidai ba don ba juyin mulkin soja ba ne, amma wani tanadi ne a kundin tsarin mulkin kasar.
Ya yi watsi da jita-jita na neman wasu kudade na jihar Ribas, inda ya kara da cewa babu wanda zai iya kwace tsarin siyasar jihar.
“Babu wanda zai iya bani tsoro, idan ina son yin wani abu zan yi, tsige shi ba juyin mulkin soja ba ne, an tanada shi a karkashin tsarin mulkin kasa, ba ni da sha’awar duk jita-jita, kudi, da sauransu. Sharar gida. . Sharar da ba ta dace ba, watanni nawa ne na bar ofis, kuma ni Minista ne na FCT, to wanne kudi?
Amma babu wanda zai iya kwace mana tsarin siyasarmu. Babu kowa. Ba za ku iya aiki ba kuma mutane za su fara kawo maƙiya, wwaɗanda za su yaƙe ku lokacin da kuke fafutukar ganin mutumin ya kasance a ofis. Wike ya kara da cewa kar a tabo tsarin siyasar jihar. Ba zan rufe idona in yi shuru ba.
Wike ya kuma yabawa kungiyar Gwamnonin bisa ziyarar ban girma da suka kai masa, ya kuma yabawa shugaba Bola Tinubu bisa gata da ya samu na zama ministan babban birnin tarayya Abuja, yayin da ya jaddada goyon bayan sa ga ajandar sabunta begen shugaban kasa.
Tun da farko, Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, ya gode wa Wike bisa yadda ya yi niyyar warware batutuwan, inda ya ce kungiyar ta “shiga cikin lamarin”, wanda ya nuna muhimmancin jihar Ribas. Ya kuma yaba wa shugaban kasa bisa nadin da ya yi wa Wike a matsayin ministan babban birnin tarayya, inda ya bayyana cewa magabatansa sun yi magana kan iya shugabanci.
Daga Fatima Abubakar.