OHINOYI NA AL’UMMAR IBIRA YA KWANTA DAMA

0
42
  • OHINOYI NA AL’UMMAR IBIRA YA KWANTA DAMA

Rahotanni sun bayyana cewa a safiyar yau ne, Allah ya yi wa Sarkin Al’ummar Ibira (Ohinoyi of Ebiraland), Dr. Ado Ibrahim ya rasu da safiyar yau Lahadi 29 ga Oktoba, 2023.

Wata majiya daga fadar Sarkin na Ibira, ta shedawa cewa sarkin mai shekaru 94 a duniya, ya rasu a wani asibiti da ke birnin tarayya Abuja da safiyar Lahadi, kuma za a gudanar da jana’izarsa a Okene babbar shalkwatar Al’ummar Ibira da ke jihar Kogi a yau Lahadi.

Dr. Ado Ibrahim ya zama Sarkin Ibira ne a ranar 2 ga watan Yuni, 1997. Kuma an haife shi a ranar 7 ga watan Fabrairu, 1929. Kafin zaman sa Sarkin Ebira (Ohinoyi of Ebiraland) babban ɗan kasuwa ne a jihar Legas.

 

Daga Fatima Abubakar.