BAYAN BARAZANAR EL-RUFAI, JAMI’AR JIHAR KADUNA ZATA CIGABA DA ZAMAN KARATUN

0
46

 

Hukumar gudanarwar Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta koma karatu karo na biyu na shekarar 2020/2021 ga sababbin dalibanta da tsofoffi, sama da watanni biyar bayan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi.

An sake komawa ne domin ci gaba da jarabawar semester na biyu da aka dakatar saboda yajin aikin ASUU da ya fara a watan Fabrairun na bana.

A wani jawabi da ya yi a ranar Talata, mukaddashin shugaban jami’ar jihar Kaduna, Farfesa Abdullahi Ashafa ya bayyana cewa makarantar ba ta da wata matsalar da kungiyar ASUU ta yankin, don haka babu bukatar a ci gaba da ajiye daliban a gida.

Ya yi gargadin cewa za a fuskanci mummunan sakamako ga dalibai da malaman da suka kasa komawa karatu kamar yadda hukumar jami’ar ta umarta.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho